An kai hari da makamin roka kan sansanin sojin Amurka na Aynul Asad da ke Iraki.
Kakakin Kawancen Sojin Kasashen Duniya da ke yaki da 'yan ta'addar Daesh karkashin jagorancin Amurka Kanal Wayne Marotto ya shaida cewa,
"Da misalin karfe 14.45 ne aka kai hari da makaman roka guda 3 kan sansanin Aynul Asad. Makaman rokar sun fado a harabar sansanin. Babu wata asara ko jikkata da aka samu."
Marotto bai fadi su waye suka kai harin ba, haka zalika bai baiyana ko an mayar da martani ba ga harin ba.