An kai hari da makamai masu linzami 4 samfurin Katyusha a yankin da ofisoshin jakadancin kasashen waje suke a Bagdad Babban Birnin Iraki.
Kafar Yada Labarai ta Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iraki ta fitar da sanarwa ta shain Twitter cewa a daren Juma'ar nan ne aka kai harin da makamai masu linzami samfurin Katyusha guda 4 a yankin.
Ba a samu asarar rai ko dukiya ba sakamakon harin.
Sanarwar ta ce an kai harin daga wani waje da ke kusa da sansanin sojin Al-Rashid da ke kudancin Bagdad, kuma jami'an tsaro sun kwace injinan da aka harba makaman da su.
A yankin da aka kai harin akwai ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama da suka hada da na Amurka.
Ana yawan kai hari da makamai masu linzami samfurin Katyusha kirar Iran a yankin.