Mutane 6 wadanda 5 daga cikinsu yara ne sun mutu a wani harin da aka kai da bindiga kan wani gida a garin Muskogee da ke jihar Oklahoma ta Amurka.
A cewar sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, ‘yan sanda sun je wurin ne saboda harbin bindiga da aka ji daga wani gida. Yayin da suka gamu da wani dauke da bindiga a gidan, ‘yan sanda sun tsare wanda ake zargi da ya ke kokarin tserewa.
An bayyana cewa, an gano mutane 5, 4 daga cikinsu yara kanana, sun mutu a gida, kuma an kai yaro 1 da mace asibiti da raunuka.
Bayan hakan, an bayar da rahoton cewa yaron ya mutu a asibiti kuma matar har yanzu tana cikin mawuyacin hali.
‘Yan sanda ba su bayar da cikakken bayani game da wanda ake zargi ba, amma sun sanar da cewa ana kan bincike.