An kai hari a wani babban kanti a Amurka

An kai hari a wani babban kanti a Amurka

Mutum 1 ya rasa ransa yayinda wasu hudu suka samu raunuka sakamakon hari da bindiga da aka kai wani babban kanti da ke jihar California ta Amurka.

'Yan sanda sun bayyana cewar maharin ya kutsa kai kantin rarraba kaya ga 'yan sari inda ya bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wani mutum mai shekaru 45 Martin Haro-Lozano ya rasa ransa inda wasu 4 kuma suka jikkata.

'Yan sanda sun harbe maharin mai shekaru 31 wanda a baya ya taba yin aiki a kantin.


News Source:   www.trt.net.tr