An sanar da kaiwa sansanin sojan Amurka dake Taci a arewacin babban birnin Iraki Baghdad hari da makami mai linzami.
Dangane ga bayanan da suka fito daga kafafafen yada labaran kasar Iraki masu alaka da tsaro an kai hari da makamai masu linzami biyu a sansanin sojan Amurka dake Taci a arewacin Baghdad.
Ba'a dai samu hasarar rayuka a harin rokan da aka kai akan sansanin sojan Taci inda sojojin Iaraki suke ba.
Rubutacciyar sanarwar ta kara da cewa dakarun kasar Amurka da na Iraki sun fara bincike akan lamarin.