An kai hari a ofishin jakkadancin Faransa a Saudiyya

An sanar da cewa an kaiwa wani jami'in tsaro hari da wani abu mai kaifi a ofishin jakadanjinFransa dake kasar Saudiyya.

Bayan harin an sanar da kame mutum daya.

Kamar yadda kanfanin dillancin labaran Saudiyya ta SPA ta sanar an kaiwa wani jami'in tsaro hari da abu mai kaifi a ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Jiddah.

An kara da cewa an kame wani mutum mai shekaru 40 da laifin kai harin.

Mai magana da yawun ofishin 'yan sandan yankin Makkah a kasar Muhammed el-Gamidi ya shaidawa manema labarai da cewa an garzaya da wanda aka kaiwa harin asibiti.

El- Gamidi ya kara da cewa za'a fara bincike akan lamarin.


News Source:   ()