An kai hari a kusa da ginin kotun kolin Brazil

An kai hari a kusa da ginin kotun kolin Brazil

A Brazil wani mutum da ya yi damara da abubuwa masu fashewa ya mutu a gaban ginin kotun kolin kasar a jiya laraba.

‘Yan sanda dake sintiri a wajan sun ce sun hango  wata mota na ci da wuta yayin da hayaki da turnike sararin samaniya kahin daga bisani wani mutum ya fito cikin gaggawa daga motar.

Rahotanni sun ce fashe-fashen sun afku ne a kusan lokaci daya ba tareda sun jikkata ko da mutum guda ba. Kakakin fadar shugaban kasar Brasil ya ce shugaba Lula ba ya a fadar sa lokacin afkuwar fashe-fashen.

Wanan dai na faruwa ne yayin da kasar ke shirin karba taron kasashe masu karfin tattatlin arziki a duniya na G7.

Rana 8 ga watan Janairu 2023 mako guda bayan dawowo Lula akan kujera mulki, wasu magoya bayan tsofan shgaban kasa Jair Bolsonaro suka kutsa kai a ginin da ke kunshe da manyan hukumomin kasar uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)