A wani hari da aka kai da wuka a filin tashi da saukar jiragen saman Dusseldorf dake kasar Jamus mutun daya ya raunana.
Kamar yadda mujallar Focus ta sanar, maharin ya ari na kare jin kadan bayan kai harin.
Harin da kawo yanzu ba'a san musabbabinsa ba an kai shi ne a sashen da matafiya suke a filin jirgin.
An bayyana garzayawa da wanda ya ji raunin zuwa asibiti mafi kusa.