An kai hari harin bindiga a babban ofishin ýan sandan dake Jakarta babban birnin kasar Indonesia.
A babban ofishin ýan sandan dake Kudancin Jakarta babban birnin kasar Indonesia ne wani da aka zargin dan ta'adda ne ya budewa mutane wuta.
An yi nasarar kashe maharin sai dai ba a bayyana ko wanene ba. Wadanda lamarin ya afku akan idonsu sun bayyana cewa akwai wani mahari guda amma ya tsere daga yankin.
A yayinda yan sanda suka kewaye yankin an kara karfin tsaro a yankunan baki daya.