A Siriya fararen hula 7 sun samu raunuka a harin makami mai linzami da gwamnatin Assad ta kai kan wani yanki da kuma tashar ajiye motoci a Idlib.
A cikin sanarwar da aka fitar a shafin Twitter na Ma’aikatar Tsaron Kasar Turkiyya, an bayyana cewa gwamnatin da ta kai hari kan wata asibiti a Idlib, a wannan karon ta kai hari da makamai masu linzami kan gundumar Kah da ke Arewacin Idlib da kuma wurin shakatawa na TIR kusa da Sarmada.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa fararen hula 7 sun samu raunuka a wurin shakatawar TIR kuma dabbobi da yawa na mutanen kauyen Kah sun mutu.
An kara da cewa "An sanar da Tarayyar Rasha game da dakatar da kai hare-hare nan take. An kuma gargadi sojoji. Ana kuma bin ci gaban lamurkan.”