A kalla matasa masu goyon bayan demokradiyya 10 da jami'an tsaro 23 ne suka jikkata sakamakon rikicin da aka gwabza a lokacin da masu zanga-zanga suka kusanci ginin bataliya ta 1 da Firaministan Tailan Prayut ya ke zaune a ciki.
An bayyana cewa, an yi amfani da harsashan roba da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka tsallake shingayen jami'an 'yan sanda domin shiga ginin.
Bayan da sojoji suka kwace mulki a shekarar 2014, aka nada Prayut a matsayin Firaministan gwamnatin Tailan wadda "Majalisar Zaman Lafiya ta Kasa" ke jagoranta.
An dauki tsawon shekaru 5 an dage lokacin zabe a kasar, amma bayan wata doka da sojojin suka yi, an gudanar da zaben a shekarar 2019.
Masu adawa da gwamnatin Tailan sun fara gudanar da zanga-zanga a ranar 14 ga Disamban 2019 bayan zaben da ake takaddama a kai.