Mutane 7 sun jikkata sakamakon harin bindiga da aka kai a garin Philadelphia na jihar Pennsylvania da ke Amurka.
Majiyoyin yankin sun shaida cewa, an kai hari da bindiga a kusa da cibiya ababan hawa na gwamnati da ke yankin Olney a arewacin Philadelphia.
An bayyana jikkatar mutane 7 sakamakon harin, ba a bayar da wani dogon bayani ba game da wadanda aka jikkata.
An bayyana kama wanda ya kai harin.
'Yan sanda sun kwace bindigu 2 , kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.