Mutane 6 sun jikkata sakamakon hari da bindiga da aka kai a garin Bryan na jihar Texas da ke Amurka.
Labaran da jaridun Amurka suka fitar na cewa, wasu daga cikin wadanda aka jikkata na cikin halin rai mutu kwakwai.
'Yan sanda sun je wajen da lamarin ya afku, kuma har yanzu ba a kama wanda ya kai harin ba.