Mutane 2 sun samu raunuka sakamakon hari da wuka da aka kai a garin Erfurt na kasar Jamus.
Lamarin ya afku da safiyar Litinin din nan inda aka kai mutanen da aka jikkata masu shekaru 45 da 68 zuwa asibiti.
An bayyana cewa, 'yan sandan Jamus sun fara sintiri da jirgin sama mai saukar ungulu don kamo maharin da ya gudu bayan kai harin.
Sanarwar farko da aka fitar ta ce, maharin na da kimanin shekaru 20.
A ranar Juma'ar makon da ya gabata ma an kai hari da wuka a garin Wurzburg na Jamus tare da kashe mutane 3.