Mataimakin Shugaban Kasar Afganistan na Daya Amrullah Salih ya samu rauni a hannunsa, sakamakon harin bam da aka kai wa jerin gwanon motocinsa.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Tarik Aryen ya shaidawa manema labarai cewar, an kai harin bam din a lokacin da Salih yake wucewa ta yankin Taiman da ke Kabul Babban Birnin Kasar.
Aryen ya ce Salih ya kubuta da ransa amma ya samu rauni a hannunsa, an kuma kashe mutane 2 tare da jikkata wasu 12 sakamakon harin na bam.
A gefe guda, Mataimakin Shugaban Kasar Afganistan na Daya Salih ya fitar da sanarwa ta shafinsa na sada zumunta inda ya ce "Na ji ciwo a hannuna, kuma wannan hari ba zai hana ni yaki da ta'addanci ba."
Gilasan gidajen da ke kusa da wajen da aka kai harin sun farfashe, an kuma rufe dukkan hanyoyin da ke zuwa wajen.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.