An ji karar fashewar wasu ababe a garin Kudus dake yammacin Tahran babban birnin kasar Iran.
Kafar talabijin gwamnatin kasar ta sanar da cewa ba'a bayyana musabbabin fashewar wani abu da aka ji kararasa ba a garin Kudus dake karkashin gundumar Germdere a jihar Elburz.
An dai tabbatar da yankewar wutar lantarki jin kadan bayan lamarin ya afku.
A 'yan makonnin da suka gabata yawan fashewar ababe da ake samu na bututun iskar gas da taransfoma a kasar Iran ana ikirarin cewa suna da nasaba ga harin yanar gizo da ake kaiwa kasar daga waje.