An yankewa Firaiministan Norway Erna Solberg tarar kroner dubu 20,000 wanda ya yi daidai da dallar Amurka ($2,350) akan laifin karya dokar bayar da tazara da aka saka a kasar domin yaki da kwayar cutar Korona.
Kamar yadda hukumar 'yan sandan kasar ta sanar, Solberg ta gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta a ranar 27 ga watan Febrairu tare da halartar mutane 13 a wani gidan abinci da ya nuna sun karya dokar nisantar juna da aka saka domin dakile yaduwar Covid-19.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Ole Saeverud ya bayyna cewa "Duk da dai dokar daya ce ga kowa, ba duka ne ake dai-dai a gaban doka ba“
Ya kara da cewa, ya zama wajibi a saka tarar domim a nunawa al'umman kasar irin karfin dokar nisantar juna da aka saka domin yaki da Korona.
Dangane ga dokar hana yaduwar COVID-19 a Norway ba'a yarda fiye da mutum 10 su kasance a gidan cin abinci daya a lokaci guda ba.