An bayyana kai hari da makaman roka 10 kan sansanin sojin Amurka na Ayn Al-Asad da ke jihar Anbar din kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labarai na Iraki da ya sanar da kai harin, bai bayyana su waye suka kai harin da kuma ko an samu a sarar rayuka da dukiya ba.
Gwamnatin Iraki ma ba ta ce komai ba game da batun.
A ranar 26 ga watan Disamban 2018, tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya kai ziyarar bazata sansanin sojin Ayn Al-Asad da ke Anbar.