Firaiministan Vietnam Nguyen Xuan Phuc ya bayar da umarnin dakatar da shigowa dama cinikin dabbobin daji a cikin kasarsa domin kara tsaurara matakan kare yaduwar kwayar cutar Covid-19.
Sanarwar ta bayyana cewar dokar ta kunshi hana shigo da dabbobin daji a mace ko a raye da kuma hana farautarsu tare da hana siyar dasu a kasuwannin kasar.
Vietnam ta kasance kasar da yankin Asiya ke yawan shiga da naman dabbobin daji da ma dabbobin dajin da ransu ba tare da bin ka’ida ba. Daga cikin naman dajin da ake shiga dasu kasar sun hada da na giwaye, dabbar Pangolin da kahon dabar rhino.