An haifi jaririn da garkuwar jikinsa ka iya yaki da Covid-19 a Bulgaria

An haifi jaririn da garkuwar jikinsa ka iya yaki da Covid-19 a Bulgaria

Likitoci a Bulgaria sun tabbatar da cewa an haifi wani jaririn da garkuwar jikinsa ka iya yaki da kwayar cutar Covid-19 dake ci gaba da addabar duniya.

A ranar 5 ga watan Janairu ne dai wata mata 'yar shekaru 28 mai suna Yordanka Brandiyiska ta haifi jariri mai kilo 2 da giram 750 a garin Pazarcik dake kudu maso gabashin kasar Bulgaria wanda aka tabbatar da cewa garkuwar jikinsa ka iya yaki da kwayar cutar Korona.

Wani abin mamaki dai mahaifiyar jaririn ta kasance wacce ta kamu da kwayar cutar Korona a lokacin da cikin jaririn ke wata bakwai.

Brandiyiska, wacce aka yiwa aikin tiyata domin fitar da jaririn gudun kada ya kamu da kwayar cutar na Korona ta bayyana farin cikinta ganin jinjirin nata nada garkuwar da ba zai iya kamuwa da annobar ba.

 


News Source:   ()