An sanar da shigar da karar shugabanin mujallar barkwanci ta charlie hebdo akan zanen tozarcin da suka yiwa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
An bayyana cewa an kai karar daraktan mujallar, shugaban kula da rubuce-rubuce da editan mujallar karar zanen batancin da suka yiwa shugaba Erdogan.
Wadanda suka shigar da karar sun nemi a hukunta wadanda suka yi zanen batancin akan shuagabn kasar Turkiyya.