Syria wadda ta yi yaƙin fiye da shekaru 10 ko da ya ke anga lafawar yaƙin a shekarar 2016 lokacin da aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin ƴan tawayen da ke yaƙi da dakarun gwamnati, alƙaluma sun nuna yaƙin a matsayin mafi ɗaiɗaita jama’a.
Ƴan ƙasar ta Syria fiye da miliyan 10 ne suka tsere ƙetare da kaso mai yawa a ƙasashen Turai daban-daban musamman a ƙasashen irin Jamus da Faransa da New Zealand, sai dai kawar da gwamnatin Assad ya sanya wasu daga cikinsu tunanin komawa gida don ci gaba da rayuwa tare da haɗuwa da sauran ƴan uwa waɗanda yaƙin ya tagayyara.
Turkiya da ke maƙwabtaka da Syria na sahun ƙasashen da ke ɗauke da tarin ƴan ciranin Damascus waɗanda yaƙi ya tilastawa barin gida, sai dai a hukumance, gwamnatin Ankara ba ta fara mayar da su gida ba, face waɗanda suka yi gaban kansu wajen komawa.
Ma’aikatar harkokin wajen Turkiya ta ce tarin ƴan Syria sun fara tururuwar komawa gida kuma wannan adadi na mutum dubu 7 da 600 sun fice daga Istanbul ne a tsakanin ranakun 3 zuwa 9 ga watan nan.
Sai dai komawar ƴan ƙasar gida na zuwa ne a wani yanayi da hankula bai kammala kwantawa ba, bugu da ƙari kuma ake fargabar bama-baman da gwamnati ta birne a ƙarƙashin ƙasa su iya yin illa ga jama’a musamman a yankunan da suka jima ba mutane a ciki.
Tuni dai kiraye-kiraye suka fara yawaita ga gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria ƙarƙashin jagoranci Abu Mohammed al-Julani wajen ganin ya yi hoɓɓasa tare da gaggauta fara aikin cire bama-baman waɗanda ke birne a ƙarƙashin ƙasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI