Wasu gungun masu zanga-zanga a Baghdad, babban birnin Iraki, sun yi zanga-zangar rashin tasirin ayyukan gwamnati da kuma karuwar kashe-kashen fararen hula masu fafutukan kare hakkin bil adama a kwanankin nan.
Masu zanga-zangar da suka taru a dandalin Nusur da ke Bagadaza sun kalubalanci gwamnati game da kisan masu fafutukan kare hakin bil adama tare da neman da a kamo masu kisan kuma a hukunta su.
Wasu matasa sun rinka nuna hotunan wasu 'yan gwagwarmaya da kuma allonan da aka rubuta "wa ya kashe su?"
Masu zanga-zangar a Iraki sun kuma rera taken kalubalantar Iran da Amurka akan katsalandan da suke yi a kasar.
An gudanar da kamfe mai yawa a shafukan sada zumunta domin zanga-zangar ta yi tasiri.
An kashe masu fafutuka da suka jagoranci zanga-zangar kwanan nan, musamman a biranen kudancin Iraki.