An gudanar da zanga-zanga a Italiya don nuna adawa da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gabashin Kudus da Gaza.
A Milan, birni na biyu mafi girma a Italiya, an gudanar da zanga-zanga wadanda kungiyoyi daban-daban suka shirya, musamman Falasdinawa.
Kusan mutane 3,000 ne suka hallara a dandalin Duomo da ke tsakiyar garin, suna mai da martani game da tsoma bakin Isra’ila da hare-hare da take kaiwa Falasdinawa a Gabashin Kudus da Zirin Gaza.
An daga tutocin Falasdinu a yayin zanga-zangar, kuma an yi shiru na minti guda domin jimami wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren Isra'ilan.
Masu zanga-zangar sun yi ihu "Intifada", " Yanci ga Falasdinu ", "Isra'ila' yan ta'adda".
A hare-haren sama, da sojojin Isra’ila suka kai wa Gaza wanda ya fara a ranar 10 ga watan Mayu kuma ya ci gaba duk da Bikin Ramadan, yara 28 da Falasdinawa 119 ne suka yi shahada sannan 621 suka ji rauni.