An gudanar da zanga-zangar "Babban Ayarin Kudus" a Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus (TRNC) don nuna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kan Falasdinawa.
Daruruwan motoci sun shiga ayarin da ƙungiyoyi masu zaman kansu 12 suka kafa a babban birnin kasar, Nicosia tare da halartar mutane da dama.
An bayyana cewa mahalarta taron sun daga alluna da taken "Bada murya ga mamaya" kuma suna dauke da tutar Turkiyya, TRNC da na Falasdinu.