An gudanar da bukukuwan ranar 15 ga Yuli a Amurka

An gudanar da bukukuwan ranar 15 ga Yuli a Amurka

A ranar cika shekaru 4 da kawar da yunkurin juyin mulki na 'yan ta'addar Fethullah (FETO), motocin a-kori-kura da jiragen sama dauke da hotunan abubuwan da suka faru a ranar sun zaga a tituna da sararin samaniyar wasu jihohin Amurka.

A aiyukan da aka yi karkashin Kungiyar Turkawa Mazauna Amurka, an ja hankalin Amurkawa da motoci da jiragen sama dauke da manyan hotunan ranar 15 ga Yulin 2016.

A jikin manyan hotunan an rubuta "15 ga Yuli, Nasarar Demokradiyyar Turkiyya" da "Nasarar Al'ummar Turkiyya", kuma motocin sun zagaya manyan tituna a yankunan Manhattan, Brooklyn da Queens da ke birnin New York da kuma Washington DC da ma kewayen gidan da SHugaban FETO yake zaune a jihar Pennsylvania.

Jiragen sama dauke da rubutun "Ku dakatar da dan ta'addar FETO" sun daukitsawo rana guda suna zagaye a sama.


News Source:   www.trt.net.tr