Ma’aikatar matasa da wasanni ta kasar Turkiyya ta gudanar da “Concert” a dandalin Sultanahmet a yayin bikin cika shekaru 568 da kafa birnin Istanbul.
Shahararrun masu zane-zane sun dauki fage tare da shahararrun ayyukansu a bikin, wanda kuma ya samu halartar Ministan Matasa da Wasanni Mehmet Muharrem Kasapoglu.
Bayan jawabinsa, Ministan Kasapoplu ya kalli kade-kade da wake-waken da matasan suka gabatar.
A karshen dare, duk masu zane-zane sun rera taken nasara tare da Ministan Matasa da Wasannin Kasapoglu.
Bikin wacce ta dauki tsawon awanni 3, an watsa ta kai tsaye a tashar TRT Music, da tashar TRT ta kamfanin Rediyo da Talabijin na Turkiyya, da kuma kafafen sada zumunta na Ma’aikatar Matasa da Wasanni.