An gano wata sabuwar nau’in Coronavirus a Singapore

An gano wata sabuwar nau’in Coronavirus a Singapore

Masana kimiyya da fasaha a kasar Singapore sun sake gano wata sabuwar nau’in kwayar cutar COVID-19.

 Mujallar The Lancet Medical ce ta rawaito hakan inda ta bayyana cewar wacannan sabuwar cutar bata kai coronavirus tasiri da karfi ba, sai dai bulluwar ka iya haifar da kalubale ga yunkurin samar da allurar riga-kafin Covid-19 da ake yi.

Binciken ya nuna cewa masu fama da corona da suka kamu da sabuwar kwayar cutar ta SARS-CoV-2 zasu iya samun sauki cikin sauki ba tare da bukatar kulawar gaggawa ba.

Haka kuma garkuwar jikinsu zata kasance mai karfi. Binciken dai ya kunshi cibiyoyin kiwon lafiyar kasar Singapore da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Yaduwa Cututtuka ta (NCID) a kasar da kuma makarantar kiwon lafiya ta Duke-NUS da Cibiyar Kimiyya da Fasahar kasar.


News Source:   ()