Masana ilimin sararin samaniyya a Amurka sun sanar da gano wasu duniyoyi 24 da suka radawa suna "superhabitable " da za'a iya rayuwa a cikinsu.
A kafar yanar gizon "TechExplorist" aka yada cewa da jagorar masanin sararin samaniyya Dirk Schulze-Makuch na Jami'ar Washington wasu kungiyar masana ilimin sararin samaniyya sun gano wasu duniyar da suka fi duniyarmu tsufa, girma, sanyi da kyawon yanayi wadanda za'a iya rayuwa a cikinsu.
Masanan sun yi bincike cewa duniyar dake wajen rana da za'a iya rayuwa a cikinsu nada nisan light years 100 daga duniyar da muke ciki.