An gano wani sabon nau'in kwado a Ostreliya

An gano wani sabon nau'in kwado a Ostreliya

Masana kimiyya na Ostreliya sun gano wani sabon nau'in kwado wanda ake kira "kwadon chocolate” a dazukan da ke tsibirin New Guinea.

Masanin kimiyya Steve Richards ne ya gano wannan kwadon, wanda ake kira "Litoria mira", a shekarar 2016, amma sai da aka kwashe shekaru ana bincike kafin aka tabbatar da cewa nau'in dabbar sabo ne.

An san kwadin bishiyoyi da koren fata, amma lokacin da aka gano Litoria mira saboda launin fatansa mai kama da chocolate, sai aka yi masa lakabi da "kwadon chocolate”.


News Source:   ()