An gano wani babban kabari dauke da gawarwaki 20 a lardin Salahaddin da ke kasar Iraki.
Kyaftin Ahmet Ekrem daga ofishin ‘yan sanda na Salahaddin ya bayyana cewar a yankin karkara da ke kusa da wani kauye a kudancin lardin, an samu manyan kaburbura yayin da rundunar ‘yan sanda ke sintiri.
Da yake bayyana cewa har yanzu ba a san wanda suka kashe mutanen da aka gano ba, Ekrem ya ce wasu gawarwakin suna da alamun duka da harsasai kuma lamarin ya haifar da zargi kan cewa kungiyar ta'adda ta DAESH ce ta aikata lamarin.
Ekrem ya kara da cewa an fara bincike kan lamarin.