An gano mutane biyu a kasar Sabiya da ke daube da salon "Delta" na sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19), wanda aka fara gani a karon farko a Indiya kuma ya fi saurin yaduwa.
A cikin sanarwar da Ma’aikatar Kiwon Lafiyar kasar ta fitar, an bayyana cewa marasa lafiyan da ake magana a kansu sun dawo kwanan nan daga kasashen waje.
An lura a cikin sanarwar cewa mutanen ba sa cikin mawuyacin hali kuma an gano cewa mutanen ba su karbi allurar riga-kafin Covid-19 ba.”
A cikin sanarwar, an kuma lura cewa an binciki samfurori da aka dauka daga marasa lafiyan a Cibiyar Kula da Lafiyar Dabbobi ta Kraljevo.