An gano sabon bidiyon yadda 'yan sandan Amurka ke amfani da karfin da ya wuce kima

An gano sabon bidiyon yadda 'yan sandan Amurka ke amfani da karfin da ya wuce kima

An gano sabon bidiyo da ke dauke da yadda 'yan sandan Amurka ke amfani da karfin da ya wuce kima wajen zaluntar bakaken fata.

'Yan sandan garin Clayton sun tsayar da wani bakar fata mai suna Roderick Walke saboda bai kunna fitilar tsayawa ba a motarsa.'Yan sandan sun bukaci Walker da ya sakko daga motar tasa tare da nuna katin shaidar zama dan kasa.

Da Walker ya tambayi ko me ya sa hakan, sai 'yan sandan suka kayar da shi.

'Yan sandan sun ci gaba da maguza shi duk da ihun fadin "Bana Iya Numfashi" da buruwarsa ke yi, da kuma kiran "Babana" da 'yarsa ke yi.

An kori dan sandan da ya aikata wannan zalunci.


News Source:   ()