An gano wani sabon nau'in malam buɗe littafi yayin binciken da aka gudanar a Dutsen Ararat da ke Turkiyya.
A karkashin aikin da Sashen Bincike na Jami’ar Igdir ya tallafawa, an gudanar da wani bincike kan wani nau'in malam buɗe littafi a yankin Igdir kuma an gano wasu sabbin nau'ika.
Sakamakon binciken da aka kwashe tsawon shekaru 3 ana gudanarwa, kungiyar daga Jami’ar Igdir karkashin jagorancin Dakta Celalettin Gozuacik ta gano wani sabon nau'in malam buɗe littafi wanda ba a taɓa gani ba.
Kungiyar binciken sun yi rajistar sunnan sabon nau'in malam buɗe littafin a matsayin Ancylosis Igdirensis (Ancylos Igdir).
A yayin aikin, an kuma gano wasu nau'ika 12 wadanda a da ba a yi musu rajista a Turkiyya ba.