An gano sabbin halittu 12 a cikin Tekun Atlantika

An gano sabbin halittu 12 a cikin Tekun Atlantika

An gano wasu sababbin nau'ikan halittun ruwa 12 a cikin Tekun Atlantika.

Sabbin halittun da masana kimiyya suka gano wadanda suka kwashe tsawon shekaru 5 suna bincike a Tekun Atlantika a zaman wani bangare na aikin Atlas, ya haifar da farin ciki.

Sakamakon binciken an gano wasu nau'ikan halittun 12 da ba a taba gani ba, ciki har da sabbin nau'ikan algae, mollusk da murjani.

Wadannan nau'ikan ba a taba gano su ba har sai yanzu saboda rashin isasshen bincike a kasan tekun.

Kungiyar ta kuma gano sabbin alamomi na nau’ika 35 da ke rayuwa a wuraren da aka sani a baya.

Wadannan sabbin nau’ikan halittun da aka gano suma suna fuskantar barazanar canjin yanayi. Yawan adadin iskar carbon dioxide a cikin teku yana kara yawan sinadirin acid a cikin ruwan kuma musamman murjani a cikin ruwan sun fara rubewa a sakamako.

Farfesa Murray Roberts daga Jami'ar Edinburgh wanda ya jagoranci aikin ya bayyana cewar binciken ya kuma bayyana wasu yankuna na musamman a cikin tekun. Ya ce,

Mun sami yankuna masu zurfi a ruwa na soson ruwa da murjani a tekun. Wadannan yankuna na tallafawa rayuwa a cikin teku. Kifaye na yin ƙwai a waɗannan yankuna. Idan waɗannan yakunan sun lalace ta hannun dan adam, waɗannan kifayen ba za su sami wurin da za su yi kwai ba kuma waɗannan halittun da ke cikin tekun ba za su rayu ba a nan gaba.


News Source:   ()