An gano kwayar halittar da zata hana sauro sanya zazzabi

Published by:   , Default Admin

An gano kwayar halittar da zata hana sauro sanya zazzabi

Masana kimiyya da fasaha sun bayyana yin nasarar gano wata kwayar hallitar da zata iya hana saura sanya ciwon zazzabi.

Dangane ga kafar yada labaran BBC, tawagar masana kimiyya da fasaha dake gudanar da ayyukan bincike a kasashen Birtaniya da Kenya akan yadda za’a magance matsalar zazzabin cizon sauro dake salwantar da dubun dubatan rayuka a ko wace shekara sun gano wani abu mai muhimmanci da dadin ji.

A binciken da suke yi akan saurayen dake tabkin Victoria dake kasar Kenya; sun gano wani kwayar halittar da suka radawa suna "Microspora MB" wanda zai hana saurayen iya samu da yada kwayar cutar dake haifar da zazzabi.

Mujallar Nature ta yada binciken da aka gudanar a dakin binciken cututtuka inda ta tabbatar da cewa wacannan kwayar halittar mai suna "Microspora MB" ka iya kare da kange sauro daga iya daukar kwayar cutar dake haifar da zazzabi ga bil adama.

Masana kimiyya da fasahar dake kan nazarin yadda za’a iya yada wacannan kwayar halittar ga mafi yawan sauraye a doron kasa; suna kuma nazarin ko hakan ka iya kawo karshen zazzabin cizon sauro baki daya ko kuma a’a.

Dangane ga binciken da suka gudanar za’a iya yada saurayen da suke dauke da wacannan kwayar halittar ga dukkan sauran sauraye, da haka za’a iya kawo karshen matsalar zazzabin cizon sauro.


News Source:   www.trt.net.tr