An gano kwayar cutar kyandar biri a Amurka

An gano kwayar cutar kyandar biri a Amurka

An sanar da cewa an gano kwayar cutar kyandar biri a wani fasinja Ba'amurke da yo taso daga Najeriya zuwa birnin Dallas da ke jihar Texas a Amurka.

Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka (CDC) ta sanar da cewa an gano wani Ba’amurke da ya sauka a Filin jirgin saman Dallas daga Najeriya a ranar 9 ga watan Yulin na dauke da kwayar cutar kyandar biri kuma an kwantar da shi a asibiti.

Alkalin Gundumar Dallas, Clay Jenkins ya bayyana cewa "Babu wani yanayin tashin hankali kuma ba ma tsammanin wata babbar barazana."

Jami'ai sun bayyana cewa hadarin yaduwar kwayar cutar da ake magana a kai ba ta da yawa, yayin da fasinjoji ke sanya ababen rufe fuska a cikin jirage saboda sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19).

Kwayar cutar kyandar biri, wacce aka fara ganowa a birrai a cikin dakin binciken a shekarar 1950, tana yaduwa ta hanyar numfashi kuma tana iya yaduwa daga mutum zuwa mutum kuma ba a gan ta a Amurka ba na tsawon shekaru 20.

Alamomin cutar, wadanda ke bayyana tsakanin kwanaki 7 zuwa 14, sun hada da gajiya, ciwon kai, zazzabi da ciwon jiki.

Babu takamaiman magani ko allurar riga-kafi ta cutar wacce aka shawo kanta a cikin 2003.


News Source:   ()