An gano jirgin saman Rasha samfurin AN-28 da ya bata dauke da mutane 17.
An bayyana cewa, mutanen da ke cikin jirgin na nan kalau.
Kafafan yada labarai na Rasha sun bayyana cewa, jirgin samfurin AN-28 ya tashi daga garin Kedroviy zuwa Tomsk inda bayan bayar da alamar gaggawa a yankin Bakcharsky sai aka neme shi aka rasa.
A binciken da aka gudanar an gano jirgin ya do a inda bai shirya ba kuma dukkan mutanen cikin sa nan kalau.