A garin Salvatierra da ke jihar Guanajuato na kasar Mekziko an gano jikkunan mutane 59 binne a rami 1.
Shugaban Hukumar Bincike na Kasa Karla Quintana ya ce a makon da ya gabata ne aka gano wasu ramukan da aka binne mutane.
Ya zuwa yanzu an ciro jikkunan mutane 56 a yankin, kuma mafi yawan su matasa ne da kuma mata.
Ana ci gaba da aiyukan bincike a yankin.