An gano jakunkuna 18 dauke da sassan jikin mutane a Mexico

An gano jakunkuna 18 dauke da sassan jikin mutane a Mexico

An gano wasu jakunkuna har guda 18 dauke da sassan jikin mutane da suka hada da kasusuwan bil adama a jihar Jalisco ta Mexico.

An bayyana gano jakukunan a garin Zapopan dake jihar Jalisco wacce ta kasance jihar da aka fi samun yawan fitinu a kasar.

Mai gabatar da kara a jihar ya bayyana cewa kasusuwan mutane da saura sassan mutane da aka gano cikin jakukunan ba za'a iya gane ko na mutane nawa bane, amma tuni an aika dasu asibiti domin yin bincike.

Mai bayar da shawara akan harkokin kare hakkin dan adam da kuma yawan al'umman kasar Alejandro Encinas, ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2006 zuwa 2021 kiminanin mutane dubu 82 sun bace a kasar Mexico.

An bayyana kungiyar "Sabbin Zamanin Jalisco" a matsayar kungiyar da ta fi aikata ayyukan fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

A kasar Mexico fiye da mutane dubu 300 sun rasa rayukansu tun daga shekarar 2006 da aka kaddamar da yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Kimanin mutane dubu 40 suka ɓace a wannan lokacin inda kuma  sama da 340 Mexicans suka yi ƙaura daga matsugunansu.


News Source:   ()