An bayyana cewa an gano burbushin kifi da ake kira "saber anchovy" masu shekaru milyan 45 a kasar Pakistan.
Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gidan Pakistan suka rawaito a rafin Rakhi dake garin Dera Gazi Han dake da nisan kilomita kilomita 700 daga teku masu bincike sun gano wasu burbushin kifi da suka radawa suna "Churel"
Mai bincike Alessio Capobianco a sashen yanayin da duniya a jami'ar Michigan dake jagorantar binciken da kwamitinsa ke yi ya bayyana cewa irin wannan kifin ya yi kama da na wanda suka gano a Beljiyom kwanakin baya.
Wannan burbushin kifin da aka gano a Pakistan yana da girman mita daya kuma ana tsammanin yakai shekaru miliyan 45 wanda aka radawa suna "Monosmilus Chureloides" daga kalmomin Girka daya da Jordan anchovy.
Binciken ya kara da cewa ana kuma hasashen cewa kifin ya kasance yana rayuwa a wani tekun yankin kasar Pakistan.