An sanar da gano wani babban kabari da aka binne uwa, baba da yaransu biyu a kudancin Tripoli babban birnin Libiya bayan an kubutar da yankin daga hannun mayakan Janar Haftar.
Danagane da sanarwar ma'aikatar cikin gidan Libiya a shafinta na sadar da zumunta a yankin Aziziye dake kudancin babban birnin kasar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Libiya ta bayyana sanar da jami'an tsaro wani babban kabari da ta gano a yankin Saadiye da aka kubutar daga hannun mayakan Janar Haftar 'yan tawaye masu tada kayan baya.
Ana zaton cewa gawawwakin na wasu iyalai ne da aka bayyana sun bace a watan Nuwamban shekarar 2019.
Sojojin Libiya, wadanda suka kawar da dakarun Hafter daga sansanonin Vatiyye dake yammacin kasar a ranar 18 ga watan Mayu, suna kuma ci gaba da tsarkake yankunan yammacin kasar daban-daban daga mayakan.