An magance karin 'yan ta'addan PKK/YPG hudu a yankin da aka kaddamar da farmakin tafkin zaman lafiya a Siriya.
Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar da hakan a shafukanta na sadar da zumunta. Inda take cewa,
"Jaruman dakarun kasarmu sun gudanar da farmakai a yankin da aka kaddamar da farmakin tafkin zaman lafiya. Sun kuma yi nasarar magance mambobin 'yan ta'addan PKK/YPG dake neman hana zaman lafiya a yankin"