A ranar Talatar nan aka fara yin allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) a Ingila.
An fara yi wa Margaret Keenan mai shekaru 90 allurar riga-kafin da kamfanunnukan Pfizer da BioNTech suka samar.
Keenan da ya rage mako 1 ta shiga shekara ta 91, ta karbi allurar a asibitin yankin Coventry da ke Ingila.
A karon farko, za a yi wa mutane dubu 400 allurar riga-kafin.
An fara yin allurar a manyan asibitocin Ingila.
An bayyana cewar za a yi amfani da wasu filayen wasanni don yin allurar riga-kafin. Jaka zalika wasu shagunan sayar da magunguna da kananan asibitoci ma za su shiga aikin.
A karon farko, an kai alluran asibitoci 50 na Ingila, ana kuma ajje su a waje mai sanyin -70.
Ta yanar gizo ana bibiyar allurar na Pfizer-BioNtech da aka tura Ingila daga kasar Beljiyom.
Za a yi kashi na farko na allurar da bayar da hutun kwanaki 21.
Za a fara yi wa masu shekru sama da 80 da ke gidan kula da tsofaffi, ma'aikatansu da ma'aikatan lafiya.
Ana hasashen cewar makonni masu zuwa za a yi wa Sarauniya Elizabeth mai shekaru 94 da mijinta Yarima Philip mai shekaru 99 allurar.
A Ingila, mutane dubu 61,434 annobar Corona ta kashe kuma adadin wadanda suka kamu ya kai mutane miliyan 1 da dubu 737 da 960.
A gefe guda, ana ci gaba da mayar da martani ga matakan yaki da cutar da ake dauka.
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da suka yi kokarin shiga wani babban kanti da ke Ingila da kuma rufe hanyoyin ababan hawa.
'Yan sanda sun kama masu zanga-zanga 4.