
Hukumomi Masar da suka tabbatar da zaman tattaunawar, gabanin cikar wa'adin zangon farko na ranar Asabar, sun bayyana fatan cimma matsaya ta dindin da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ya yi ajalin dubun dubatar Falasɗinawa.
Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar, ya ce tawagar Isra'ila ta jima da isa Masar, domin ganin ko akwai sahihiyar matsayar tattaunawa kan tsawaita yarjejeniyar.
Ana ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar farko, bayan da Isra'ila ta saki fursunonin Falasdinawa 46, ciki har da yara 24, bayan da aka samu jinkiri wajen tantance gawarwakin mutane hudu da Hamas ta mika wa gwamnatin ta Yahudu.
Wani bincike da sojojin Isra'ila suka gudanar a kan hare-haren da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba, 2023, ya amince da gazawar sojojin ƙasar wajen daƙile abin da suka kira mummunan harin da ya kashe gomman mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI