An fara taron addini mafi girma a duniya da mutum miliyan 400 ke halatta

An fara taron addini mafi girma a duniya da mutum miliyan 400 ke halatta

Makwannni 6 ko sama da haka mabiya addinin Hindi za su kwashe a wannan taro na Maha Kumb da mutane miliyan 400 ke halatta

Mabiya addinin na taruwa a mahaɗar wasu manyan koguna 3 da suka haɗar da Ganges da Yamuna da Saraswati. Za su haɗu domin ayyukan ibada na mabiya addinin Hindi.

Mabiya addinin na girmama kogunan musamman na Ganges da Yamuna.

Sun yi imanin cewa duk wanda ya yi wanka cikin ruwan za’a goge masa dukkanin zunuban da ya aikata ta yadda zai dawo tamkar ranar da aka haifeshi.

Galibin masu halattar taron na share dukkan kwanaki inda suke yin wanka a lokacin da rana ke fitowa.

Sheikh Saaliq wakilin kamfanin dillanci labarai na AP ya ce taron na bana zai ƙara fito da ƙima ta shugaban India bisa yadda ya bai wa addinin Hindi da al’adun India muhimmancin.

Taron addini mafi girma a duniya 01:28

Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies

Amince Zabin son raina Taron addini mafi girma a duniya AP - Rajesh Kumar Singh

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)