An fara shirin tsige gwamnan New York akan laifin cin zarafin mata

An fara shirin tsige gwamnan New York akan laifin cin zarafin mata

Kafafen yada labaran kasar Amurka sun shagaltu akan lamarin da ake zargin gwamnan birnin New York  Andrew Cuomo da cin zarafin mata.

Tuni dai am fara daukar matakan cire gwamanan daga mukaminsa.

Shuagaba majalisar New York Carl Heastie, ya bayar da izinin fara zaman tsige gwamna Andrew Cuomo da laifin cin zarafin mata 6.

Gwamna Andrew Cuomo, wanda mata 6 suka zarga da musgunawa ya zuwa yanzu, ya kasance wanda ya yi ko oho da kiran "murabus" din da ake yi masa.

Shugaban Jamiyyar Democrat a zauren majalisar kasar Sanata Chuck Schumer ma ya yi kira ga Cuomo da ya yi murabus.

 


News Source:   ()