An sanar da mayar da gwawarwaki sarakuna 18 da na matan sarakuna 4 wadanda aka adana gangan jikinsu daga birnin Alkahira zuwa garin Fustat.
Kamar yadda jaridar Ahbar al-Yevm ta sanar tashin mai taken "tafiyar zinari" hadi da sarki Ramses na biyu za'a sauyawa sarakuna 18 da sarauniyoyi hudu da aka adana gagan jikkunansu daga Gidan Adana Kayan Tarihin Alkahira zuwa na garin Fustat.
Kamar yadda jaridar El-Mısri el-Yevm ta rawaito taron ya samu halartar gidajen talabijin da kafafen yada labarai na kasa da kasa har 40 wanda kuma mashhuran 'yan wasa kamar su Muna Zeki, Ahmed Hilmi da Huseyin Fehmi suka halarta.
Shugaban Gidan Adana Kayan Tarihin Misira Ahmed Ganin ya bayyana cewa wannan ne mataki na farko akan shirin tattara gagan jikkunan sarakunan Misira guri guda.
Ma'aikatar harkokin yawon bude idon Misira ta bayyana cewa gagan jikkunan sarakunan tun na shekarar 1871 da 1898 ne wadanda aka gano a kudancin kasar.
Haka kuma sun kasance a karkashin tsarin mulkin Fir'auna a shekara 1580 da 1085 gabanin milladiyya.