An fara sauraren kara domin hukunta wadanda suka kashe Jamal Khashoggi

An fara sauraren kara domin hukunta wadanda suka kashe Jamal Khashoggi

Turkiyya ta fara gudanar da shari’a akan ‘yan kasar Saudiyya 20 akan kashen dan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya dake Istanbul.

Babban mai gabatar da kara ya shirya takarda mai shafi  117 wanda aka gabatar gaban babban koton sauraren miyagun laifuka akan kisan Khashoggi Jamal da aka yi.

An fara sauraren karar ne a babban koton Caglayan Courthouse dake Istanbul.

An dai kashe Khashoggi ne jin kadan bayan ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya dake Istanbul a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2018.


News Source:   www.trt.net.tr