Jagoran adawa a ƙasar ta Isra’ila Yei Lapid ne ya yi kira ga Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi murabus daga muƙaminsa bayan ajiye aiki da babban Hafsan sojin ƙasar Herzi Halevi ya yi.
Ya ce murabus ɗin da babban hafsan sojin Isra’ila ya yi ya nuna ƙarara cewa lokaci ya yi da ya kamata Firaministan ƙasar ya fito fili ya ɗauki laifinsa tare da yin murabus daga kan mulki.
A yau talata ne dai babban hafsan sojin Isra’ila Herzi Halevi ya sanar da cewa zai yi murabus daga kan kujerarshi a ranar 6 ga watan Maris, inda ya tabbatar da cewa gazawarsu ce ta janyo Hamas ta samu damar kutsawa Isra’ila a wani mummunan hari da ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Halevi zai kammala tattara bayanai dangane da harin na Hamas na 7 ga watan October tare da ƙarfafa dakarun sojin Isra’ila wurin tunkarar duk wani ƙalubale kafin ya miƙa shugabanci ga wani mutum na daban da kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba.
Babban hafsan sojin na Isra’ila ya ce zai ci gaba da kasancewa yana tuna gazawar da ya nuna dangane da harin na mayaƙan Hamas har ƙarshen rayuwarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI